Boko Haram sun arce da soja daya, ma’aikatan agaji uku a Barno

0

Wasu ‘yan bindiga da aka tabbatar Boko Haram ne, sun yi wa tawagar jami’an agaji kwanton bauna, suka arce da ma’aikata uku da wani soja daya.

Lamarin maras dadin ji ya faru ne Arewacin Jihar Barno, a ranar Talatar da ta gabata.

Jami’an na tafiya ne tare da kwamba din sojoji masu take musu hanya daga Maiduguri zuwa Monguno, a lokacin. Sai Boko Haram suka you musu kwanton-bauna a cikin Karamar Hukumar Guzamala.

Majiya ta tabbatar da cewa sun kyale direban ya koma, kuma ta hannun sa ne aka samu karin bayanin yadda lamarin ya faru.

PREMIUM TIMES ta fahimci cewa kungiyoyi sun nuna ko-in-kula, ba su ce komai ba, tun bayan arcewa da aka yi da jami’an ranar Talata.

Amma Gwamnatin Jihar Barno ta tabbatar da afkuwar lamarin. Duk da dai ba a fadi sunayen kungiyoyin da wadanda aka Kama din su biyu ke we aiki ba.

Amma Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Jihar Barno, ta ce cikon na ukun ma’aikacin ta ne.

Shugabar Hukumar SEMA ta jiharBarno, Yabawa Kolo ce ta tabbatar da haka.
Ta kara da cewa sun sanar wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro. Rundunar ‘Yan Sandan Barno da kuma Kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa, duk sun shaida wa Premium Times cewa ba su da labari.

Share.

game da Author