Bulaliyar Majalisar Dattawa Sanata Uzor Kalu, ya bayyana a Zauren Majalisa a ranar Talata, mako guda bayan sallamar say daga kurkuku.
Mai Shari’a Mohammed Idiris na Babbar Kotun Tarayya ne ya daure shi shekaru 12, bisa tuhumar zambar kudade naira bilyan 7.1, mallakar Jihar Abia.
Kalu ya yi Gwamnan Jihar Abia, daga 1999 zuwa 2007. Kuma tun cikin 2007 din aka fara tabka shari’ar sa, sai cikin Janairu 2020 aka yanke masa hukunci.
Ranar 8 Ga Mayu, Kotun Koli a karkashin wasu alkalai 7, sun soke hukuncin da aka yi wa Kalu tare da Use Udeogu, wanda aka daure su tare.
Udeogu shi ne Daraktan Harkokin Kudade na Gidan Gwamnatin Abia, a lokacin da Kalu ke gwamna a jihar Abia.
Kotun Koli ta ce an daure Kalu ba bisa ka’ida ba, kamar yadda lauyoyin sa suka daukaka kara cewa, Mai Shari’a Idris na Babbar Kotun Tarayya, ya daure Kalu wata daya bayan an daga likkafar sa zuwa gaba, wato ya zama Mai Shari’a a Kotun Daukaka Kara Ta Tarayya.
A kan haka ne lauyoyin Kalu suka daukaka karar kin amincewa da daurin shekaru 12 da aka yi masa, suka zarce har Kotun Koli.
Alkalai bakwai na Kotun Koli sun ce Dokar Kasa ba ta yarda Alkalin Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ya koma ya yanke hukunci a Babbar Kotun Tarayya ba.
Ganin cewa Kotun Koli haramta hukuncin kawai ta yi, amma ba ta ce a saki Kalu ba, sai lauyoyin sa suka garzaya Kotun Daukaka Kara, suka nemi a sake shi, tunda dai Kotun Koli ta ce daurin da aka yi masa haramtacce ne.
Mai Shari’a Mohammed Liman na Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, Lagos, ya bada umarnin a saki Kalu.
Jami’an Gidan Kurkuku sun bi umarnin kotu, suka sake shi washegari.
Yayin da ya shiga Zauren Majalisa, Shugaban Majalisar Dattawa ya yi masa maraba lale , tare da Kiran sa Bulaliyar Majalisar Dattawa.
Discussion about this post