Kungiyar Likitocin Najeriya (NARD), wadda ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, ta ce barazanar da gwamnatin tarayya ta yi wa mambobin ta ba zai sa ta janye yajin aiki ba, har sai an biya wa kungiyar bukatun da ta gindaya wa gwamnati tukunna.
Ranar Talata ce Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce ko dai likitocin su koma bakin aikin su, ko kuma a daina biyan su duk ranakun da ba su je aiki ba, har said ranar da suka koma sannan a fara lissafin fara biyan su.
NARD ta maida wa Gwamnatin Tarayya kakkausan martani, ta hannun Shugaban Kungiya Aliyu Sokomba, wanda ya ce, “wannan furuci na gwamnati shirme ne, holoko kuma wasan kwaikwayon da shekara dari baya, gwamnati ba ta taba yin irin sa ba.”
Sokomba ya ce su fa babu wata matsala tsakanin su da gwamnati, sai neman cika musu bukatar su uku, a wannan lokaci da ake fama da cutar Coronavirus.
Dalilan Yajin Aikin Likitoci:
Sokomba ba ya ce su na bukatar gwamnati ta biya su dukkan albashin da ba a biya su ba.
Sannan kuma akwai kudaden alawus-alawus na shiga hatsarin da suke yi, musamman yanzu wajen kula da marasa lafiya, yayin cutar Coronavirus. Amma gwamnati ta ki biyan su.
Bukatar su ta uku kuma ita ce, ba sau daya ko sau biyu ba, sun sha yi wa gwamnati korafi da kukan karancin kayan kariya ga likitoci don gudun kamuwa cutar Coronavirus, amma har yanzu dai likitocin sun ce kayan na karanci, kuma rayuwar su na cikin barazana.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Mayu ne gwamnati ta tabbatar da cewa sama da likitoci da jami’an kula da lafiya sama da 800 ne suka kamu da cutar Coronavirus.
Sannan an samu rahotannin mutuwar wasu likitocin a jihohi da dama.
Wannan dalilin da ma wasu dalilai ne likitoci su ka yanke shawarar tafiya yajin aiki, domin gwamnatin tarayya ta bar rayuwar su cikin hatsaei a lokacin da su likitocin ke kokarin dakile cutar Coronavirus.
Jama’a da dama sun cika da mamaki jin cewa likitoci sun fantsama yajin aikin rashin kayan kariya da rashin biyan su hakkokin su.
Hakan kuwa a cewar wasu da dama sa su ka rika yin tsokaci a shafukan su na twitter da Facebook, su na mamakin ne ganin yadda a kullum gwamnati na yin sanarwar bilyoyin kudaden da ta ce ta na kashewa a bangaren yaki da cutar Coronavirus da kuma bilyoyin da ta ce ta na kashewa wajen bayar da tallafun jin kai, kayan agajinabinci makudan kudaden da ta ce ta kashe wajen ciyar da dalibai a gidajen su, yayin zaman dirshan a gida, saboda cutar Coronavirus.
Discussion about this post