Babu jihar da Korona bata dira ba a Najeriya – NCDC

0

Shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya yi ikirarin cewa babu jiha ko daya a Najeriya da cutar Korona ba ta bulla ba.

Ihekweazu ya fadi haka ne a taron ‘yan jarida da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Korona ta yi ranar litini a Abuja.

Alkaluman da Hukumar NCDC ta fitar ranar 21 ga watan Yuni sun nuna cewa mutum 20,244 suka kamu da cutar a jihohin 35 da Abuja.

Hakan ya nuna cewa jihar Cross Rivers ce kadai jihar da bata cikin jihohin Najeriya da cutar ta bayyana a cikin su.

Sai dai ma’aikatar kiwon lafiya na ganin akwai lauje a nadi game da hakan.

A haka me kuma a ranar 18 ga watan Yuni a ka bayyana wani dan majalisar dokoki na jihar Godwin Akwaji ya rasu a asibitin da ake killace masu fama da cutar Covid-19 a jihar.

Ihekweazu ya ce haka ya nuna cewa akwai yiwuwar cutar ta bulla a jihar.

Bayan haka ita ma jihar Kogi ta kafe cewa har yanzu bata da wanda ya kamu da cutar a jihar, tana mai cewa mutanen da ake ce sun kamu da cutar a jihar ba gaskiya bane.

Ya ce ko kasar New Zealand dake kusa da teku da a da babu cutar yanzu ta kamu.

Daga nan kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya yi kira ga mutane da su rika zuwa yin gwajin cutar a wuraren da aka bude a fadin kasar nan.

Ya ce don mutum shikenan zai mutu kenan, a sani a yi magani da wuri yafi a yi ta buya har sai ya kai ga ba za a rayu ba.

Share.

game da Author