Ba a sanar da ranar da za a bude wuraren horas da dalibai ‘yan NYSC ba – Hukuma

0

Hukumar Jin dadin dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa ba za a bude sansanin dalibai masu yi wa kasa hidima ba tukunna.

Jami’ar yada labaran Hukumar Adenike Adeyemi ta Sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.

Ta ce babu gaskiya wa wannan labari da ake ta yadawa cewa gwamnati zata bude sansanin.
Adenike ta ce za a bude sansanin idan gwamnati ta bada umurin a bude.

“Ba Za a bude sansanin masu bautan kasa ba idan ba mun tabbatar da kare dalibai daga kamuwa da cutar Korona a lokacin da ake horas da su a sansanonin kasar nan.

Ta yi kira ga mutane da su daina sauraran irin wadannan labarai domin babu gaskiya a cikin su.

Adenike ta ce za a iya samun bayanai na Hukumar a shafinsu dake hangar gizo.

Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Maris ne hukumar NYSC ta dakatar da horas da dalibai masu yi wa kasa hidima na Rukunin A na shekarar 2020 a duk sansanonin Najeriya.

Hukumar ta kuma raba wa daliban wasikun tura su wuraren da za su yi aikin yi wa kasa hidimma.

NYSC ta yi haka ne domin kare dalibai daga kamuwa da Korona da yada ta.

Share.

game da Author