Fadar shugaban kasa ta jadda kololuwar zumunci, son juna da aminantakar dake tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jagoran jam’iyyar APC Bola Tinubu cewa suna na kamar takalmin kaza, mutu ka raba.
Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehuda ya bayyana haka a wata takarda ranar Asabar.
” Ku sani ko a lokacin da ake kafa jam’iyyar APC, shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Bola Tinubu ne suka jagoranci kafa wannan jam’iyya, sun hadu dukkan su akan ginshikin gina kasa wanda ‘yan Najeriya za su yi alfahari da ita. Sun toshe kunnuwar su daga sauraren magulmata wadanda aikin su kitsa makircine da hada husuma ne.
” Suna nan tare tamau gam-gam, kuma suna tuntubar juna akai-akai. Aminantakar da ke tsakanin su sai su, babu wanda zai Iya shiga tsakani.
Jagorarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a karon farko tun da jam’iyyar APC ta shiga cikin runani da ya kai ga shugaba Muhammadu Buhari ya wancakalar da kwamitin gudanarwar jam’iyyar, Tinubu ya bayyana matsayar sa game da halin da jam’iyyar ta shiga.
” Maimakon mu dawo mu hada kai mu sasanta kan mu, kowa ya fallo takobin sa sai yadda yake so dole za ayi ko kuma ba za a zauna lafiya ba. Sannan wasu kuma siyasa ce ma a gaban su na burin da suka dashi.
” Abin mamaki har da wadanda ma tare da su aka aza tubalin gina wannan jam’iyya. Kowa ya manta gwagwarmayar da akayi har da wanda aka yi a 2019. Tsohon shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya taka rawar gani matuka a zaben 2019 tare da sauran mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar. Inda kuma aka yi kuskure, dama mutum 9 ne bai cika 10 ba.
” Ita kanta kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta rufta cikin hayaniyar da babu gaira babu dalili. Maimakon a sasanta a tsakani sai sai kowa ya nade kafar wandon sa ya garzaya kotu. Abin ma ya zama kamar wani wasan yara, kullum sai tabarbarewa yake yi.
” Shugaba Buhari ba amfana kawai yayi da jam’iyar APC ba, ya ba da dinbin gudunmawarsa sosai a samun ci gaban ta. Abin da yayi haka ko wani uba zai yi idan ‘ya’yan sa suka ki sasanta tsakanin su.
” Na bauta wa jam’iyyar APC da duka karfi na, kamar yadda wasun mu suka yi. Ina kira ga mambobin jam’iyyar da suka fusata da hukuncin da kwamitin zartaswar jam’iyyar ta yanke da rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Burin da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suke da shi ya dara soyayyar da suke wa jam’iyyar da ya sa kowa da ta sha mai kai sai ya garzaya kotu.