Ba a bude wuraren ibada da kasuwanni ba, ayi hattara – Gargadin gwamnatin Kaduna

0

Gwanmatin Kaduna ta gargadi mutanen jihar cewa kada su kuskura su bude masallatai da coci da kasuwanni domin dokar jiha ce ta saka ba gwamnatin Tarayya ba.

Mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar ranar Talata a madadin gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

” Jihar Kaduna ba ta cikin jihohin da gwamnatin tarayya da saka dokar hana walwala a ciki. Saboda haka babu dalilin da zai sa dokar gwamnatin tarayya ya yi aiki a jihar tunda ba ita ta saka dokar ba.

” Muna yi wa mutanen jihar gargadin cewa kada wani ya kuskura ya bude masallaci ko coci da zumman yin sallah, ko wata ibada, haka kuma Kasuwanni. Har yanzu doka na nan daram na hana sallah a masallatai da ibadar Coci sannan kuma kasuwanni za su ci gaba da zama a garkame.

” Gwamnati zata ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na bangaren addini da shugabannin kasuwanni kamar yadda ta bayyana a jawabin mataimakiyar gwamna zuwa har a tsara yadda za a bude garin daki-daki.

” Jihar Kaduna ta tsara yadda za ta bude gari wanda ya sa ta kara kwana daya na walwala a makon jiya sannan kuma gwamnati tana tattaunawa da kungiyoyin yan kasuwa da da sauransu domin a tsara yadda za a bude gari ta yadda ba za a koma gidan jiya ba.

Gwamnati ta yi kira ga mutanen jihar su maida ci gaba da bin doka kamar yadda gwamnati ta saka a jihar da ya hada da dokar hana zirga-zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe. Sannan kuma dokar hana tafiye-tafiye na nan daram. Jami’ai na nan a iyakokin Kaduna domin kam wadanda suka karya doka da kuma biyan tara daga kotun tafi da gidan ka.

Share.

game da Author