Audu Maikori ya lallasa gwamnatin Kaduna a Kotu, za ta biya shi miliyan 10

0

Kotun daukaka kara a Abuja ta jaddada hukuncin da babban kotun Abuja ta yanke gwamnatin Kaduna ta tauye wa fitaccen mamallakin kamfanin Chocolate City Audu Maikori damar da yake dashi na walwala na tsare shi da tayi, bayan jami’an tsaro sun jijjibo shi tun daga Legas zuwa Kaduna a 2017.

Kotun ta tabbatar da hukuncin babbar kotu da ta yanke hukunci irin haka a baya kafin gwamnatin Kaduna ta daukaka kara.

Sai dai kuma kotun ta rage kudin tara da babban kotu ta saka akan gwamnatin Kaduna inda tace sai ta biya Maikori naira miliyan 40 na tauye masa hakki da tayi zuwa miliyan 10.

A yanayi na murna, Maikori ya saka labarin nasasar da yayi a kotun daukaka kara kan gwamnanatin Kaduna.

Idan ba a manta ba Maikori ya maka gwamnatin Kaduna a kotu, inda ya roki kotu ta tilasta wa gwamnan jihar Nasir El-Rufai da gwamnatin jihar ta biya sa naira biliyan 10 a dalilin tauye masa hakki da tayi a 2017.

Shi dai Maikori ya fada hannu gwamnatin El-Rufai ne bayan ya saka wani rubutu a shafin sa ta tiwita da daga baya abinda ya rubuta ya zamo ba haka bane.

Gwamnatin Kaduna ta sa an tsare shi na kwanaki hudu kafin a aka kai shi kotu, inda daga baya kotu ta bada belin sa,

A dalilin haka ne sai maikori ya garzaya Kotu ya nemi abi masa hakkin sa na tsare shi da aka yi na kwanaki ba tare da an kai shi kuto. Ya bukaci gwamnati ta biya shi diyyar naira biliyan 10.

Duka alkalan da suka yanke hukuncin a kotun daukaka kara sun amince da hukuncin kotun farko, cewa lallai an tauye wa Maikori hakki na walwala.

Share.

game da Author