APC za ta lashe zaben Edo, Ondo sannan mu kwace Anambra mu hada – Yahaya Bello

0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya jaddada cewa ko tantama baya yi cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zabukan gwamnoni dake tafe a kasar nan.

Bello ya bayyana haka ne bayan ganawa da kungiyar kwamnonin yankin Arewa Maso Tsakiya da suka yi da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari.

Manema labarai sun tattauna da shi bayan sun kammala ganawar a fadar shugaban kasa.

” Ina so kusa ni cewa ita ma jihar Anambra za mu jijjibo ta daga PDP ta dawo APC idan lokacin zabe yayi. Muna so ‘yan uwan mu Inyamirai su zo mu sha lagwadan tare.

” Jihar Edo kuwa da ita ke gaban mu da Ondo. Za mu lashe su kamar kwankwadar ruwan sanyin mai jin matsanancin kishi, farad-daya za mu yi musu a wuce wurin.

Da aka tambaye shi baya tsoron ko karfin kujerar mulki ta yi wa Obaseki tasiri a zaben jihar, Bello ya ce babu tasirin da za ta yi masa.

” Duk da ban ji dadin canja sheka da Obaseki yayi ba, hakan ba zai sa mu daga masa kafa ba, zai sha kayi ne kawai, domin APC ce zata ci gaba da mulki a jihar. Kowa ya ga yadda Buhari ragargaza PDP a zaben baya duk da sune a kan mulki. Haka ma yanzu babu wani tasiri da zai yi masa.

Share.

game da Author