Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar Hukumar Shelleng Lazarus Bakta a jihar Adamawa.
Wani ma’aikacin karamar Hukumar ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.
Ma’aikacin ya ce an yi garkuwa da Bakta a gidan sa dake kauyen Bakta da misalin karfe 1:20 na ranar Talata.
Wani mazaunin kauyen ya ce maharan sun arce da Bakta da karfe 2 na ranar Talata.
“Maharan sun shigo kauyen mu dauke da manyan bindigogi suna harbi sama don firgita mutane.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari yana mai cewa rundunar da ‘yan farauta a kauyen za su fantsama dazukan yankin domin ceto Bakta.