An kama matashin da ya yi wa gyatuma ‘yar shekara 70 fyade, bayan ya gudu ya bar wando, a dakin ta

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun sun tabbatar da kama wani mai shekaru 25, mai suna Wasiu Bankole, bayan ya yi wa wata tsohuwa mai shekaru 70 fyade.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimnola Oyeyemi ya ce an yi wa gyatumar fyade a gidan ta da ke Ijoko, cikin Sango Ota.

“Ita ce ta kai rahoto a Ofishin ‘Yan Sanda da ke Abule Lemode, ta ce an yi mata fyaden a ranar 2 Ga Yuni, wajen karfe 8 na safe.

“Ta ce wani makwabcin ta ne da ya ji kukan ta, ya je ya bugi kwarton da sanda. Daga nan ya arce.

“Ta tabbatar cewa ya gudu ya bar wandon sa, takalmi da cocila. Amma DPO na Shiyyar Agbedo, SP Kuranga Yero ya bada umarni ka kamo shi aka tsare.

“Wasiyyu ya yi wa ‘yan sanda bayanin cewa sharrin giya ce da ya sha ya yi mankas ya kai shi ga yi wa tsohuwar fyade.

Yayin da ‘yan sanda ke rike da wando, takalmi da cocilar Wasiu a matsayin shaida, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ce a maida batun a hannun Hukumar Hana Safarar Jama’a da Dakile Laifukan Cin Zarafin Yara.

Share.

game da Author