Gwamnatin Tarayya ta sanar da bude filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, dake Abuja.
A ranar Asabar jirgi ya tashi daga filin bayan tsauraran matakai da aka saka domin kare mutane daga kamuwa da yada Korona.
Wani wakilin kamfamin dillancin labaran Najeriya da aka yi abin a idonsa ya ruwaito cewa an kakkafa wuraren yin gwajin yanayin mutum, sannan an samar da man tsaftace hannaye da ruwan wanke su.
Kowani fasinja sai ya kiyaye sharuddan da aka saka kafin ya dare jirgi zuwa koma ina ne.
Sannan kuma ko a cikin jiragen an rarraba wuraren zama. Wasu an saka ba a zama a nan saboda a samu tazara tsakanin matafiya.
Haka kuma an saka wasu manyan na’urori da za su rika tantance fasinja da mutane a filin jirgin saman.
A baya dai gwamnati ta shaida cewa zata bude tashoshin jiragen saman kasar nan ne a watan Agusta.