Akwai hadarin gaske bude makarantu yanzu – Kungiyar Malaman jami’o’i

0

Shugaban Kungiyar malaman jami’o’in kasar nan (ASUU) Biodun Ogunyemi ya yi kira ga gwamnati ta dan dakata da maganar bude makarantun kasar nan.

Ogunyemi ya fadi haka ranar Litini a hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Ya yi kira da a maida hankali wajen tsara matakai na kawar da matsalolin da ake fama da su a fannin ilimi a kasar nan kafin a bude a makarantu.

“Da dama cikin makarantun kasar nan ba su da fili a cikin harabar makarantar da za a iya bada tazarar mita 2 a tsakanin dalibai.

“Wasu masu makarantun ba su da ruwan fanfo wanda makarantun Za su iya samar da sabulu domin dalibai su rika wanke hannu a lokacin da ya kamata.

Ogunyemi ya ce a dalilin haka yake cewa bude makarantu a wannan lokaci zai iya yana da hadarin gaske a kasar nan domin makarantu basu da kudaden da za su kashe domin samar da abubuwan kare lafiyar dalibai.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ware kudade domin tallafawa makarantun kasar nan kafin ta bada umurnin bude makarantu a kasar nan.

Ya yi kira ga gwamnati da ta sanar da masu makarantu irin abubuwan da za su saka da kakkafa na kare lafiyar dalibai kafin a bude makarantu.

Share.

game da Author