ADAMAWA: Dan sanda ya bindige dan acaba da yaki bashi cin hancin Naira 100

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta damke wani dan sanda da ya kashe dan acaba da ya hana shi cin hancin Naira 100.

Kofar Richard Zaphet ne ya aikata wannan mummunar abu a kauyen Wuro-ba Adamu dake karamar Hukumar Maiha ranar Litini.

A wannan rana Zaphet ya tsare wani dan acaba mai suna Arabo Tambajam dake da shekaru 20 a shingen da ake tsare motoci da babura domin yin bincike kafin su wuce.

A wannan shinge na ‘yan sanda Kofur Zaphet ya bukaci Tambajam ya bashi cin hancin Naira 100 kafin ya wuce. Wannan matashi ya ce ba shi da naira 100 da zai bashi. Cikin fushi kofur Zaphet ya karkato Kan bindigar sa ya dirka masa a ciki.

Ko da a kai dan acaba asibiti, ya riga ya rasu.

Kakakin rundunar Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar haka yana mai cewa rundunar ta kama Zaphet sannan har ta fara gudanar da bincike a kai.

A dalilin abin da ya faru matasan kauyen Wuro-ba Adamu sun fusata inda suka nemi babbake wannan dan sanda da ofishin ‘yan sandan dake kauyen.

Shugaban karamar Hukumar Maiha, Idi Amin ya nuna bacin ransa Kan wannan abu da ya faru, sannan ya ziyarci marigayin a asibiti kafin ya rasu.

Share.

game da Author