A kori duk Babban Hafsan Sojan da ya kasa biya bukatar aikin da aka shi -Sanata Lawan

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya bayyana cewa ya kamata a cire duk wani Babban Hafsan da aka damka wa alhakin samar da tsaro amma abin ya gagara.

Lawan ya yi wannan furuci ne biyo bayan yadda Boko Haram suka kashe makiyaya 81 tare da banka wa kauyukan su wuta da kwashe musu shanu a Karamar Hukumar Gubio, cikin Jihar Barno.

Yayi wannan bayanin ne kafin ya kira taron gaggawa na Shugabannin Majalisar Dattawa da Shugabannin Majalisar Tarayya a ranar Alhamis.

Ya nuna rashin jin dadin yadda Majalisar Dattawa ta sha zama ta na zartas da kudirori da batutuwan yadda yadda za a samu tsaro a kasar nan.

Ya ce abin Haushi duk da kudaden da ake warewa amma har yau abin sai baya ya ke yi kamar ana shuka dusa.

Wannan kakkausan kira dai za a iya cewa ga Shugaba Muhammadu Buhari ne Sanata Lawan ya yi shi. Domin Buhari ke da ikon nadawa da kuma tsige dukkan Hafsoshin Tsaron Kasa.

An dade ana kukan cewa ya kamata Buhari ya sauke su, domin wa’adin su ya wuce tuni, kuma shekaru biyar bayan nada su, har yau a wuri daya suke tuma tsalle, maimakon a ce zuwa yanzu an magance matsalar tsaro, wadda Buhari ya yi alkawarin idan ya hau zai magance a cikin kankanen lokaci.

Sanata Abubakar Kyari na Barno ta Arewa ne ya tayar da batun kisan-kare-dangin da Boko Haram suka yi wa makiyayan, wanda ya zo daidai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da karkashe mutane a kauyukan jihar Katsina.

Kashe-kashe a jihar Katsina ya kai har wasu hakimai takwas sun yi barazanar yin hijira daga masarautun su, gudun kada a yi musu irin kisan-gillar da aka yi wa Hakimin ‘Yantumaki.

Sanata Lawan ya umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa ta gaggauta tura kayan agaji da jinkai ga iyalan mutum 81 da Boko Haram suka kashe.

Idan ba a manta ba, Majalisar Dattawa ta yi kira da a yi wa harkar tsaro gagarimin garambawul a kasar nan.

Share.

game da Author