Kakakin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, Salihu Yakasai ya yi karin bayani game da mace-macen da ake ta samu a jihar Kano a wadannan kwanaki.
A hira da yayi da Radiyon DW, Yakasai ya ce tsananin zafi ne da azabar cizon sauro ya sa mutane suke ta mutuwa a Kano amma ba cutar Coronavirus ba.
Sannan kuma wadanda suka rasu din da yawa suna dauke manyan cututtuka kamar su hawan jini, ciwon Siga da sauransu.
Ya kara da cewa, da yake asibitoci da yawa musamman masu zaman kansu ba su aiki, mutane suna samun karancin kula. hakan yasa an rika samun matsala marasa lafiya na ta mutuwa.
” Irin wadannan mutane na bukatar a kula da su na musamman, amma kuma basu samun haka saboda coronavirus, da yake asibitocin basu aiki saboda cutar.
Bayan haka kuma ya ce su fa maganar wai tsohon gwamnan jihar ya tallafawa gwamnatin jihar da wani katafaren gida domin killace masu fama da cutar coronavirus a yanar gizo suka gani. Har yanzu babu wanda ya tunkare su ya mika musu mukillan wannan gida.
” Gwamnatin mu a shirye take ta karbi duk wani gudunmuwar da za a bata domin dakile wannan cuta ta Coronavirus. Kuma ba gaskiya bane wai gwamna ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano bata bukatar gudunmawar Kwankwaso.