Watanni biyu bayan dakatar da dukkan harkokin wasan kwallon kafa a duniya, sakamakon Coronavirus, yanzu kuma an fara shirye-shiryen dawowa da wasan a kasashe daban-daban.
A Ingila an dakatar da wasan PREMIER LEAGUE a ranar 13 Ga Maris, bayan an samu kociyan Arsenal dauke da cutar Coronavirus.
Daga nan kasashen da suka fi amanna da wasan kwallo, irin su Ingila, Spain, Italy, Jamus da Faransa duk suka afka cikin annobar Coronavirus.
Cutar ta kashe dubban mutane a kasar, ciki har da masu harkokin wasan kwallo da iyalan su. Kuma ‘yan wasa da dama sun kamu da cutar.
Shirye-Shiryen Dawowar Premier League: Shugaban Shirya Gasar Premier League na Ingila, Richard Garlick, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba dukkan kungiyoyin gasar za su dawo yin tirenin domin shirin ci gaba da gasar.
Garlick ya ce amma an gindaya tsauraran matakan da kowane kulob zai rika dauka kafin da kuma lokacin yin tirenin din, domin kauce wa daukar cutar Coronavirus.
Sharuddan:
Na farko dai kowane dan wasa tilas ya sa takunkumin kare hanci da baki a lokacin da ya ke tirenin.
Su ma jami’an kula da ‘yan wasa har da kociya, tilas su daura takunkumin.
Dole kafin a fara tirenin a yi wa kowane kwallo feshin kariyar cutar Coronavirus.
Bayan an gama tirenin ma a tabbatar an yi wa kowane kwallo da raga da sauran kayan tirenin din feshin kariya daga cutar Coronavirus.
Kamfanin Kula da lafiya na CAT zai bi ‘yan wasa ya yi musu gwaji kafin ranar fara tirenin din.
Kowane dan wasa zai ajiye motar sa nesa da ta wani dan wasan. Ya kasance an bar filin ajiye motoci uku tsakanin wannan mota da waccan.
An haramta wa ‘yan wasa tofar da yawu idan ana tirenin.
Tuni dai ‘yan wasan Arsenal, Tottenham, West Ham da Brighton suka fara fita motsa jiki da na’urar motsa jiki.
Kasar Faransa ma ta fara shirin dawowa a cikin watan Yuni, amma Shugaban Kasa Edourd Phillipe ya ce kamata ya yi su dan kara tsahirtawa zuwa nan da watan Satumba.
Tuni Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta ce ranar 8 Ga Mayu za ta damka wa PSG kofi, duk kuwa da cewa ba a kammala gasar ba.
Akwai ratar maki 12 tsakanin PSG da Marsille, wadda ke ta biyu.
Sai dai kuma a Ingila ana ganin za a karasa gasar ce ba tare da ‘yan kallo ko daya ba a filayen wasa. Sai dai a kalla daga gida a cikin akwatinan talbijin kawai.
Discussion about this post