ZAMFARA: Matawalle ya koma teburin tattaunawa da shugabannin kungiyoyin da basu ga maciji da juna

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya koma teburin tattaunawa da shugabannin ‘yan bindiga da mahara da suka addabi al’ummar jihar.

Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje wasu kauyukan da mahara suka afka wa a cikin makon jiya.

Matawalle ya ce ” mun koma teburin tattaunawa da shugabannin ‘yan bundiga da suka addabi mutane domin kawo karshen hare-hare da kashe-kashen da yaki ci yaki cinyewa a jihar.

” Bana barci, har abinci ba na iya ci, tun safe har dare ina tattaunawa ne da jami’an tsaro domin kawo karshen wannan matsala na hare-hare a jihar Zamfara.

” Sannan kuma mun samu amincewar shugabannin kungiyoyin fulani dake jihar, za su yi wa sauran makiyaya bayani, su dakatar da ayyuka irin haka a jihar.

A karshe kuma ya roki mutanen jihar da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanai da zai taimaka wajen tona asirin muggan mutane dake tare da su.

Kauyukan da aka afka wa sun hada da Unguwar Rogo, Karda, Bidda da Kajera, dukkan su dake karamar hukumar Tsafe.

Jihar Zamfara na fama da ayyukan ta’addanci da hare-haren ‘yan binga. Mutane da dama sun rasa rayukan su a dalilin wadannan hare-hare.

Tun bayan rantsar da sabon gwamna Bello Matawalle, ya maida hankali wajen ganin an kawo karshen ire-iren wannan hare-hare da taki ci yaki cinyewa a jihar tun lokacin mulki Yari.

An samu nasara matuka a cikin shekara daya da darewar Matawalle kujerar mulkin jihar Zamfara.

Sai dai har yanzu akwai matsalar gaske a gaba da ake kokarin ganin an kwaranye su.

Share.

game da Author