Fitaccen ‘dan siyasar Jihar Kaduna Sanata Suleiman Hunkuyi ya gamu da fushin jam’iyyar PDP a Kaduna inda ta dakatar da shi a bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa, wato Anti-Party.
Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar Abraham Catoh ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna ranar Asabar.
A sanarwar, jam’iyyar PDP ta ce Sanata Suleiman Hunkuyi da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suna yi wa jam’iyyar zagon kasa, wadda shine dalilin da ya sa bayan ganawara kwamitin Zartaswar jam’iyyar, aka yanke hukuncin dakatar dasu daga jam’iyyar.
Baya ga Suleiman Hunkuyi da aka dakatar, akwai gogaggen dan siyasa, Ibrahim Lazuru da Dogara Mato, duk daga Karamar hukumar Lere, dake jihar.
Baya ga su akwai gogaggen malamin makaranta, John Danfulani da yayi fice wajen yin sharhi siyasa a yanar gizo.
Sannan kuma akwai Hon Hashim Garba, daga karamar Hukumar Kubau, Lawal Imam Adamu, daga karamar hukumar Soba sai kuma Ubale Salmanduna daga karamar hukumar Zaria.
Idan ba a manta ba Sanata Hunkuyi ya fice daga jam’iyyar PDP a gab da 2015, inda yabi goguwar Buhari a ya kule can cikin uwar dakan Nasir El-Rufai, da shine dan takarar gwamnan jiha Kaduna. Ba a wanye lafiya ba a tsakanin su da a karshe dai Hunkuyi, ya tattara-nasa-ina sa ya koma gidansa ta asali, wato PDP.
El-Rufai da Suleiman Hunkuyi sun yi baram-baram. A farko dai sai da gwamna El-Rufai ya tsitsine wa Suleiman Hunkuyi. Daga baya ma gwamnati ta sa aka rusa wani gidan sa da bai mallake gidan a bisa ka’ida ba.
Daga nan sai ya sake harbawa ya koma gidan sa ta asali wato, PDP kuma yayi takarar gwamnan jihar Kaduna. Sai dai kash, hakar sa bai cimma ruwa ba domin honorabul Isa Ashiru ya doke shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Ba shi kadai ba har da tsohon shugaban hukumar NEMA, Sani Sidi da tsohon gwamnan Ramalan Yero.
Suleiman Hun kuyi bai ce komai ba har yanzu game da wannan dakatarwa da jam’iyyar PDP ta yi masa a Kaduna.