ZABEN EDO DA ONDO: Yadda INEC ta tsara matakan kauce wa Coronavirus

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fitar da wani daftari mai dauke da bayanan yadda ya tsara gudanar da zaben gwamnan jihohin Edo da kuma Ondo, ba tare da jama’a sun gwamutsu har sun kamu da cutar Coronavirus ba.

Daftarin wanda ya zo hannun PREMIUM TIMES, ya nuna yadda INEC ta tsara komai tun daga ranar da za a fara maida fam na ‘yan takara, har a kammala zabe.

Wasu daga cikin matakai da sharuddan da INEC ta gindaya, sun hada da:

1. Kowane dan takarar gwamna zai cika fam din sa ya tura ta intanet, ba sai ya kwashi zugar ‘yan rakiyar sa maida fam a Ofishin INEC mai hedikwata a Abuja ba.

2. INEC za ta takaita daukar ma’aikatan zabe a cikin jihohin biyu kadai.

3. INEC za ta bibiyi Kwamitin Dakile Cutar Coronavirus na Shugaban Kasa (PTF), domin tabbatar da an gudanar da zabe bisa dokokin da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta gindaya.

4. Masu bautar kasa da za a dauka aikin gudanar da zaben, za a dauki masu aiki ne a cikin jihohin biyu da za a yi zaben kawai.

5. Za a samar wa ma’aikatan zabe da kayan kariyar kan su daga kamuwa da cutar Coronavirus yayin gudanar da zabe.

6. Za a kai sinadarin hana daukar cuta daga jikin katin zaben masu jefa kuri’a.

7. Duk wanda zai jefa kuri’a, to ya tabbatar ya je sanye da takunkumin hanci da baki. Idan babu shi, ba za a bari ya jefa kuri’a ba.

8. Ba a yadda mota kirar bas mai daukar mutum 16 ta dauki sama da mutum takwas ba.

9. Ba a yarda kwale-kwale mai daukar fasinja 14 ya dauki sama da mutum 7 ba.

10. An yarda kananan motoci su dauki mutum 2 kadai. Babura kuma fasinja 1 za su dauka.

CORONAVIRUS: Kwararan Dalilan Da Suka Hana Dage Zaben

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dalilan ta na ayyana cewa duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita a kasar nan, ba zai sa ta dage zaben gwamna ba, a jihohin Edo d Ondo.

Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya shaida wa gidan talbijin na ARISE TV cewa, INEC ba za ta dage zaben jihohin biyu ba, saboda idan ta yi haka, to nan gaba kuma za ta iya rasa wani lokaci da wata ranar da za ta shirya zaben.

Cikin watan Fabrairu ne INEC ta aza ranar 19 Ga Satumba za ta yi zaben gwamnan Edo, yayin da na gwamnan Ondo kuma a ranar 10 Ga Oktoba.

Barkewar cutar Coronavirus a Najeriya ya tilasta INEC dage zaben cike-gurabu a jihohin Bayelsa, Filato da Imo.

Ganin yadda Coronavirus ke ci gaba da fantsama a Najeriya, an rika nuna damuwar ko zai yiwu kuwa a gudanar da zabukan gwamnonin ko kuma a dage zaben.

Sai dai Kakakin INEC, Okoye, ya ce, “Dokar Najeriya ta ce a tabbatar an gudanar da zaben Gwamna daga kwanaki 150 kafin wa’adin wanda ke kai ya cika, zuwa kwanaki 30 kafin wa’adin na sa ya cika.”

Okoye ya amince da cewa Coronavirus ta kawo cikas sosai a kasar nan. To sai dai ya ce abin la’akari shi ne, an rantsar da gwamnan Edo a ranar 11 Ga Nuwamba, kuma tilas a sake rantsar da sabon kafin ranar 13 Ga Octoba. Shi kuma na Ondo a rantsar da shi kafin ranar 25 Ga Janairu.

A karshe ya nuna damuwar yadda watakila Coronavirus ba za ta bar wasu samun damar yin zabe ba. To amma ya ce INEC ta na amfani ne da abin da dokar kasa ta rattaba.

Share.

game da Author