Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Najeriya ta ce za a kwaso ‘yan Najeriya 200 da suka makale a kasar Canada.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Litini gwamnatin Najeriya ta shirya Jirgin sama Boeing 777 domin kwaso wadannan mutane ranar Alhamis.
Sai dai kuma duk dan Najeriya dake bukatan dawowa gida zai biya kudin tikitinsa na jirgi dala 1,130 da yayi daidai da Naira 452,000 zuwa dala 2,000 da yayi daidai da Naira 800,000.
Za a killace wadannan mutane na tsawon kwanaki 14 kafin su fara shiga mutane.
Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata an dawo ‘yan Najeriya 265 da suka makale a Dubai.
Amma kuma an samu rasuwar mutum daya da ya dawo daga Dubai da ya kamu da Coronavirus. An ce wannan mutum yayi fama da wasu manyan cututtuka baya ga coronavirus da yayi fama da.
Kuma a ranar Juma’a na wannan mako ne gwamnati Najeriya ta dawo da wasu ‘yan Najeriya daga kasar Birtaniya su 253.
An kuma dawo ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Amurka su 160 ranar Lahadi.
A lissafe dai adadin yawan mutanen da gwamnati ta dawo da su daga kasashen waje a makon da ya gaba ta sun kai 678.