Wani sakamakon Bincike da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya, UNFPA ta yi a Najeriya ya nuna cewa a duk shekara mata 12,000 ne ke kamuwa da matsalar yoyon fitsari a kasar.
Matsalar yoyon fitsari kan kama mace ne a dalilin doguwar nakuda ko kuma idan shekarun ta na haihuwa basu kai ta fara haihuwa ba.
Wakiliyar UNFPA, Ulla Muller ta fadi haka a tattaunawa da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai a Abuja.
Muller ta ce Najeriya na cikin jerin kasashen duniya da ciwon yoyon fitsari ta yi tsanani.
“A yanzu haka mata 148,000 ne ke fama da wannan matsala a Najeriya kuma a duk shekara sai an samu mata akalla 12,000 da suka kamu da ciwon, cewar Muller.
Ta ce UNFPA ta dade tana tsara matakai don kare mata a Najeriya daga kamuwa daga cutar.
Wadannan matakai sun hada da ilmantar da mata game da dabarun bada tazarar haihuwa, wayar da kan mutane game da ciwon da horas da ma’aikatan kiwon lafiya hanyoyin kula da masu fama da ciwon.
Muller ta ce ana warkewa daga cutar idan kwararren likita ya yi wa mace fida amma duk da haka Muller ta yi kira ga matan dake fama da wannan matsala da su rika garzayawa asibiti ana duba su akai-akai.
Ta ce UNFPA ta ce za ta hada hannu da gidajen jaridu wajen wayar da kan mutane game da matsalar a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa mata 400,000 zuwa 800,000 na fama da wannan matsala a Najeriya.
Kwararrun likitoci sun ce koda yake ana iya warkewa daga cutar ta hanyar yin aiki, amma kamata ya yi a rika bari yara na yin kwari kafin ayi musu aure sannan a rika ganin likita a duk lokacin da ake dauke da ciki.
Discussion about this post