Akalla mutum biyu ne mahara suka kashe a garin Toungo dake jihar Adamawa.
Saidai kuma mazauna garin na Toungo sun bayyana cewa mutum hudu ne aka kashe a garin ba biyu ba.
Mazaunan garin sun ce maharan sun kashe mutanen ne yayin da suke hanyar dawowa gida daga kasuwa.
“Maharan su datse hanyar da mutane ke bi zuwa gida daga kasuwa. Da zarar motan fasinjo ya iso wannan shinge na su sai su bude wa motar wuta ta ko ina.
“A dalilin haka suka kashe mutum hudu inda daya daga cikinsu ma’aikacin karamar hukumar Toungo ne.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar wannan hari inda ya tabbatar cewa nan take mutum biyu suka mutu.
Nguroje ya ce sun aika da karin Jami’an tsaro domin farautar wadannan mahara.
Ita dai garin Toungo na da iyaka da kasar Kamaru kuma a shekaru da dama tun ba yanzu akan samu rahotan yadda mahara kan tsallako daga waje ta Toungo din su shigo kasar nan.
Idan ba a manta ba ranar 14 ga watan Afrilu ‘Yan bindiga suka far wa Kauyen Kaikai inda suka kashe tsohon shugaban karamar hukumar Ganye, Sabastine Samsu Kaikai.
Bayyana sun nuna cewa Kaikai ya arce da gudu bayan maharan sun diro cikin gidan sa sai dai ba kai ga ya tsira ba suka harbe shi.