Yadda wakar ‘Coronavirus’ na Adam Zango ta saka mutane koke-koke da yin nadama a rayuwa

0

” Wannan Waka da Zango yayi Kan Coronavirus ya ratsa ni matuka. Irin Kalaman da yayi a cikin wakar har tsoron Allah zai sa ka. Sannan kuma ga karantarwar da ke ciki da kira ga mutane su tuba ga Allah.” Inji Mansur Lar, wani masoyin mawaki Zango.

Wannan sune iren-iren Kalaman da mutane suka rika yi bayan sauraren sabuwar wakar mawaki Adam Zango.

Zango ya saki wakar Coronavirus da ta karade shafukan sada zumunta a Yanar gizo.

Mutane da dama sun yaba wa wannan wake musamman Kira da aka yi a ciki na mutane su kiyaye dokokin da likitoci suka yi kira da abi don kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.

Sannan kuma ya Yi Kira ga manyan fitattun jarumai mawaka da ‘yan wasa da su taimaka wa talakawa da ke fama da tsananin talauci da rashin abinci.

Ya kuma rika tuba ga Allah kuma yayi kira ga mutane da su dage da yin istigfari da tuba ga Allah a samu saukin wannan cuta a duniya.

” Adam Zango ya kyauta matuka, musamman yadda mutane a yankin Arewa har yanzu ke ganin kamar karya ce Coronavirus. Idan irin su za su rika yin irin waka haka mai ma’ana, zai Yi tasiri matuka ga al’ummar.

Mutane sun rika yin wakar suna kwaikwayonta da fuskokin su cikin nuna nadama, wasu na kuka domin jimamin halin da aka shiga a Kasa da duniya baki daya, da tuba ga Allah.

Share.

game da Author