A sanadiyyar rikicin da ya barke a tsakanin Hausa da ‘yan kabilar Chabo dake garin Tigno, karamar Hukumar Lamurde jihar Adamawa, akall mutum 30 ne suka rasa rayukan su a wannan rikici.
Wani mazaunin garin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa rikin ya barke a sanadiyyar wani hatsarin mashin da aka yi ne a kauye.
Kusan duka gidajen wannan kauyen an babbake su kurmus.
Wani mazaunin kauyen mai suna Baba ya shaida mana cewa gwamnan jihar Ahmadu Fintiri yana ficewa daga garin, sai yan Chabo suka far musu. yace zuwa safiya Asabar, sun kirga akalla mutum 40 da suke kwance a mace.
Wani shugaban al’umma a kauyen ya ce sun bizne mutum 35 ranar Asabar.
” Ba dun Allah ya sa sojoji sun iso wannan gari daga Gombe ba da yanzu kila babu kowa ma a garin.” inji wani mazaunin Tigno