A ranar 10 ga watan Mayu wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta na yanar gizo da yake nuna wata yarinya da bata wuce shekaru 18 ba wujiga-wujiga bata cikin hayyacinta ana tattausa ta ita kuma tana kwarara kuka.
Wannan yarinya da ake ta tausawa, budurwar wani matashi ne da ya hadu da bokan sa su biyar suka yi mata fyade.
Wannan abin takaicin ya fadawa Jennifer mai shekaru 18 ranar 27 ga watan Afrilu a unguwar Narayi dake jihar Kaduna.
Shi dai wannan saurayi na Jennifer, soyayyar Facebook ne ya hadu su dawanda akan haka ne saurayin ya gaiyace ta zuwa gidansa dake Unguwar Narayi, kaduna. Isar ta ke da wuya kuwa ashe yana tare ne da wasu abokan sa a gidan.
Bayan ta shigo ta zauna sai suka buge zance daga nan kuma sai shi saurayin da abokan sa suka tilasta wa yarinyar da karfin tsiya suka yi lalata da ita.
Wani mutum mai suna Uncle Shemzz ya tausaya wa Jennifer sai ya yada wannan bidiyo a shafin sa ta Facebook.
A daidai yana kokarin yin kira ga jami’an tsaro su shiga lamarin don hukunta wadanda suka aikata wannan mummunar abu, su ko iyayen ta na can suna tattaunawa da wadannan matasa domin karbar wani abu kawai a manta da magar.
Hakan ya sa Uncle Shemzz kira ga iyayen da kada su kuskura su karbi kudi daga wadannan matasa, har sai gwamnati ta shiga wannan al’amari an hukunta su.
Kungiyoyi kare hakkin ‘yan adam sun ti tir da wannan rashin mutunci da aka yi wa Jennifer suna masu cewa sai fa inda karfin su ya kare.
tuni dai an kai Jenifer asibiti domin a bata magani kuma har an damke biyu dage cikin maza biyar din da suka ci zarafin ta.
Daya daga cikin wadanda suka afka wa Jennifer ya sahida wa ‘yan san da cewa sai da suka rika bata giya mai suna Tombo tana sha suna hira, daga nan ne suka samu sa’arta suka yi mata abin da suka yi.
A hiran da ya yi da PREMIUMTIMES wani kawun Jennifer, Joshua Benjamin ya bayyan rashin jin dadin sa ga abinda ya faru ga Jenifer kuma ya ce ba zai kyale wannan magana ba, sai an hukunta ta.