Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta bayyana cewa ta kama wani mutum mai suna Uchenna Egbuchulem mai shekaru 47 da laifin yin lalata da ‘yarsa sannan da kokarin siyar da dan dake cikinta kafin ta haihu.
Kakakin rundunar Orlando Ikeokwu ya Sanar da haka wa manema labarai.
Ikeokwu ya ce rundunar ta samu labarin wannan ta’asa da Egbuchulem ya aikata daga wajen basaraken kauyen Alaenyi Ogwa da likitan da ya kamata ya siya dan dake cikin yar ta sa.
Ya ce za a kai Egbuchulem kotu da zarar an kammala bincike.
Bisa ga bayanan da runduar ta samu ya nuna cewa Egbuchulem ya mai da ‘yarsa mai shekaru 17 tamkar matarsa inda kullun sai ya yi lalata da ita.
Mahaifiyar ‘yar ta rabu da Egbuchulem tun yarinyar na karama saboda rashin daidaituwar zaman aure.
Mahaifiyar ta koma garin su a Ivory Coast.
A duk dare kafin ya yi lalata da ‘yar ta sa sai ya lakada mata dukan tsiya sannan da yi mata barazanar guntile mata kai da gatari ko adda.
Asirin Egbuchulem ya tonu ranar da ‘yar ta gano tana da ciki.
Egbuchulem ya kai ‘yar wajen wani likita dake kauyen inda ya yi cinikin siyar da dan dake cikin ‘yarsa akan Naira 200,000.
Daga nan ne Likita ya kai yarinyar gaban sarki inda a nan ta fede musu biri daga kai har wutsiya.