Akalla likitoci 10 sun kamu da cutar Coronavirus a Asibitin Aminu Kano a lokacin da suke kokarin nemar wa majiyyata daban-daban lafiyar su.
Shugaban Kungiyar Likitocin, Abubakar Nagoma, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa likitocin sun kamu da cutar Coronavirus din lokacin da suke aikin duba lafiya da kuma ceton rayukan majiyyata, wadanda daga baya gwaji ke nuna cewa su na dauke ne da cutar Coronavirus din.
Ya ce likitoci goman da suka kamu akwai har wadanda ake bai wa horon aiki a cikin su da kuma kwararrun likitoci.
Nagoma ya ce 8 a cikin su an killace su sauran biyu kuma sun killace kan su a gidajen su, saboda babu wata alama da ke nuna sun kamu da cutar, amma kuma gwaji ya nuna cewa su na dauke da cutar.
“Akwai wasu da dama da aka yi wa gwaje-gwaje, kuma ana jiran fitowar sakamakon su a cikin wannan makon da suka kai mutum 100.
Shugaban Kungiyar Likitoci Nagoma ya ce ana bi kuma ana zakulo wadanda masu cutar suka yi mu’amala da su ana daukar jinin su domin yi musu gwaji.
Yadda Likitocin Suka Kamu
Nagoma ya nuna takaicin yadda wadannan likitocin da sadaukar da kan su suka kamu da cutar Coronavirus a Asibitin Aminu Kano. Ya ce yawancin marasa lafiya da ke zuwa asibitin ba su sanye da takunkumin rufe baki da hanci.
Sannan kuma wani musabbabin shi ne yadda wasu marasa lafiya ke boye gaskiyar ciwon da ke damun su, sai daga baya an yi musu gwaji a gano cutar Coronavirus ce.
Nagoma ya kara da cewa akwai kuma babbar matsala ta karanci ka ma rashin kayan kariya ga likitocin da ke asibitin, ta yadda takunkumin kariya ne kawai gare su, ba su sa sauran kayayyakin da aka gindaya a duniya cewa a rika samar wa likitocin da ke duba masu cuta.
“Hukumar NCDC ta ce lallai a samar wa kowane likita takunkumin baki da hanci, rufaffen takalmi, gilashin rufe idanu, hula da kuma riga da wando masu kare shi daga daukar cutar.
“Amma abin takaici duk babu wadannan da na lissafa maka, sai takunkumi kadai.
Kano ce ta biyu yanzu a Najeriya a jerin jihohi masu yawan cutar Coronavirus. Ko a ranar Litinin an kara samun sakamakon mutum 23 masu dauke da cutar Coronavirus a Kano.
Nagoma ya ce, “maganar gaskiya mu likitoci mu na fuskantar babbar barazanar karancin kayan kariya daga cuta. To amma kuma a matsayin mu na likitoci, ba za mu iya ganin marar lafiya na neman mutuwa kuma mu yi baya mu zura masa ido ba.”