Yadda Dangote ya jibge makaman yaki da Coronavirus a Kano

0

Gidauniyar Dangote Foundation (ADF) ta bai wa kamfanin 54Gene kwangilar aikin gina wuraren gwajin Coronavirus na musamman da za a rika yi wa akalla mutum 1,000 gwajin cutar a kowace rana.

Za a fara gwaji a Cibiyar Gwaji ta Dangote Foundation a ranar 10 Ga Mayu, inda za a fara da mutum 4,00 daga nan kuma a rika yi wa mutum 1000 a kullum.

Wannan katafaren aiki ya kunshu har da motocin gwaji na tafi da gidan ka da za su rika karakainar daukar majiyyata da kuma sakamakon gwajin jinin marasa lafiya.

Ba a nan Gidauniyar Dangote ta tsaya ba. Bayan kafa wannan cibiya a Asibitin Muhammadu Buhari, a Kano, ta na kuma ci gaba da ayyukan karfafa yaki da cutar Coronavirus a Kano gadan-gadan, inda ta kafa Cibiyar Killace Masu Cutar Coronavirus a Filin Wasa na Sani Abacha.

Wannan cibiya an kammala ginin ta tuni, kawai izni ta ke jira da tantancewa daga Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) da gwamnatin Kano, sai ta fara aiki.

Shugabar Kula da Gidauniyar Dangote, Zouera Youssoufou, ta ce har ila yau Gidauniyar Dangote na taimaka wa Tawagar Gaggawa ta masu zakulo masu cutar Coronavirus (RRT) da dukkan kayan da ta ke bukata domin aikin su ta tafi daidai a kan lokaci.

Sannan kuma ta yi karin hasken cewa gidauniyar ke daukar dawainiyar ingata ayyukan Cibiyar Tuntubar Bayanai kan Coronavirus a Kano.

Gidauniyar Dangote ta kara musu kayan aiki, ciki har da sabbin wayoyin kiran lambobi domin ayyukan su su tafi cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

A nasa jawabi, Gwamna Abdullahi ya gode wa Dangote, tare da bayyana cewa an samu matsalar rashin fara gagarimin yaki da Coronavirus a Kano.

“Amma a yanzu da Dangote ya jibge musu kayan aiki ga kuma zuwan Kwamitin Yaki da Coronavirus daga Gwamnatin Tarayya a karkashin Hukumar NCDC, to ya rage wa jihar Kano ta kara tashi tsaye wajen ganin an dankwafar da cutar Coronavirus a jihar baki daya.

Share.

game da Author