Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar kasa wasika ta amince masa ya ciwo bashin dala biliyan 5.513 daga wasu manyan bankunan duniya ranar Alhamis.
Shugabannin majalisun tarayya, wato na wakilai da na dattawa, Femi Gbajabiamilla da Ahmed Lawan duk sun karanta wasikar a zauren majalisa.
A wasikar, Buhari ya ce za ayi amfani da wadannan kudade ne domin cike wawukeken gibin da aka samu a kasafin kudin 2020 da kuma agaza wa wasu jihohin kasar nan na halin matsanancin rashin kudi da suka fada.
Bankunan da za a ciwo basukan da yadda za a kashe su
1 – Asusun Lamuni na Duniya, IMF –
$3,400,000,000
2 – Bankin Duniya, WB – $1,500,000,000
3 – Bankin Raya kasashen Afrika, AFDB, -$500,000,000
4 – Bankin Musulunci,IDB – $113,000,000
Za a kashe dala miliyan 125 daga za karbo daga AFDB wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan da kara maida hankali ga ayyukan dakile yaduwar COVID-19 da ake fama da. Sannan kuma dala miliyan 23 domin tallafa wa kananan manoma a wannan yanayi na annobar COVID-19.
Za a ciwo bashin dala miliyan $600 daga bankin Musulunci IDB, domin tallafawa ayyukan dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar nan.
Za a ciwo bashin dala miliyan $500 daga bankin hadahadar kasuwancin ciki da waje na Afrika domin siyan muhimman kayan aiki da magani dan aikin tunkarar annobar COVID-19.
Sai kuma Euro million €995 daga Bankin Kasar Brazil domin inganta ayyukan gona a kasar nan.
Sannan kuma wasu daga cikin wadannan bankuna ne za su samar wa jihohi basussuka domin ayyukan raya jihohin su da suka saka a gaba.
Shugaba Buhari ya shaida wa majalisar kasa cewa ya zama dole a jirkita kasafin kudin 2020 domin kudaden da aka yi tsammanin samu, ya tabbata ba za su samu ba saboda matsalar da duniya ta fada a dalilin annobar COVID-19 da maida hankali da duk duniya suka yi na ganin an gama da cutar.
Sannan kuma dole a karkatar da wasu kudaden zuwa wasu muhimman fannoni da suka jikkita saboda wannan annoba.
Wannan bashi da za ciwo ya taho a daidai makonni kadan bayan majalisar Kasa ta amince wa shugaba Buhari ya ciwo bashin naira biliyan N850bn, da kuma bashin dala biliyan 22.7 da yanzu haka yana gaban majalisar tarayya.