Gwamnan jihar Kaduna ya ce gwamnati za ta rabawa wadanda ba su iya saka katin kira na naira 200 a wata tallafin gwamnatin jihar na watan Mayu.
El- Rufai ya ce duk wanda ba zai iya saka katin kira na naira 200 a wata ba ya na neman taimako kuma sune gwamnati zata bibiya don taimakawa.
El-Rufai ya ce wannan karon ba za a samu matsalar da aka samu a baya ba. Ya ce a wancan karon wasu ne da gwamnati suka yarda da su suka yi mata ha’inci.
Ya ce wadanda kuma basu da waya kwata-kwata, za a tattauna da malamai da masu unguwanni domin nuna ire-iren wadannan mutane domin samun tallafin gwamnati.
Ya kara da cewa tuni har sun samu alkalumman mutanen da suke bukatar irin wannan taimako. Sai dai kawai kaji an kira ka an ce kazo wuri kaza ka karbi tallafin gwamnati kai tsaye.
Da yake amsa tambaya game da kokarin gwamnati game da cutar Coronavirus, El-Rufai yace gwamnati na kokarin gina sashen kula da wadanda suka kamu a duka asibitocin jihar dake kananan hukumomi 23 dake jihar.
Sannan kuma ya ce gwamnati ba za ta yi kasa-kasa wajen kare mutanen jihar daga kamuwa daga wannan cuta.