Tsohon Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya rasu

0

An tabbatar da rasuwar tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur ta Kasa (NNPC), Maikanti Baru.

Baru ya rasu cikin dare a ranar Juma’a. Har yanzu dai ba a bayyana inda ya rasu ko ciwon da ya yi sanadiyyar ajalin sa ba.

Sanarwar tabbacin rasuwar ta fito ne yau Asabar da safe, daga bakin Shugaban Hukumar NNPC, Mele Kyari. Ga abin da ya wallafa a shafin sa na Twitter dangane da rasuwar.

“Ina mai bakin cikin sanar da rasuwar dan uwa na, aboki na kuma ubangida na, Maikanti Kachalla Baru. Baru shi ne Shugaban Hukumar NNPC da ya sauka na karbi shugabanci a hannun sa. Allah ya gafarta masa, amin.”

An haifi Baru a shekarar 1959. Bayan ya yi karatu, ya fara aiki da Kamfanin NNPC, inda ya rika samun karin girma har zuwa mukamin shugaba.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada shi a cikin 2016. Cikin 2019 kuma aka cire shi, aka nada Mele Kyari a kan mukamin.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba a bayyana a Najeriya ya rasu ko a wata kasa ba

Share.

game da Author