Kungiyar Lauyoyi ta Open Bar Initiative, ta roki Shugaba Muhammadu Buhari ya yi fatali da jerin sabbin sunayen Alkalan Babbar Kotun FCT Abuja, wanda Hukumar Kula da Alkalai ta Kasa (NJC) ta fitar masa.
Sun yi zargin cewa sunayen 33 cike suke da sunayen ‘ya’yan manyan alkalan kasar nan, wadanda kuma ba su cancanci a nata su alkalai ba.
Sun yi korafin cewa matsalar Buhari ya bari harkar shari’a a Najeriya ta koma harkar gado, daga iyaye bayan sun sauka a nada ‘ya’yan su, ko za a zubar da kima da nagartar shari’a, kotuna da alkalai a kasar nan.
Cikin takardar da suka tura wa Shugaba Buhari a ranar 6 Ga Mayu, wadda Silas Onu, Chidi Odinkalu da wasu lauyoyi su biyar suka sanya wa hannu, sun ce ba za su taba bari a maida shari’a harkar gado a kasar nan ba.
Kungiyar ‘Open Bar Initiative’ ta kuma aika da kwafen wasikar ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.
Sunayen ‘Ya’Yan Manyan Alkalan Da Ke Ciki
1. Hafsat Abba-Aliyu, mai shekaru 42, ‘yar Uwan Abba Aliyu. Mai Shari’a a Kotun Koli.
2. Njidella Nwosu-Iheme, mai shekaru 36, ‘yar Mai Shari’a a Kotun Koli, Mary Odili.
3. Fatima Abubakar-Aliyu, ‘yar tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Kasa, Zainab Bulkachuwa.
4. Mimi Katsina-Alu, ‘yar tsohon Babban Jojin Tarayya, Marigayi Katsina-Alu.
5. Ibrahim Mohammed, dan gidan tsohon Grand Khadi na FCT, Abuja.
Baya ga wadannan sunayen ‘ya’yan manyan alkalai, kungiyar lauyoyin ta ce akwai kuma wasu sunayen da aka saka saboda kusancin su da manyan Hukumar Kula Da Alkalai ta Kasa (NJC).
Sunan da ya fi kara fusata kungiyar shi ne sunan Olupola Olufolashade, wadda suka ce da farko ma kwata-kwata babu sunayen ta, kuma ba a yi tantancewar da ita ba. Ba a san yadda aka yi ba wani ya bankara sunayen, ya rubuta na ta sunan a ciki.
Sun ce wanda ya tsarma sunan Olufola a Kotun Koli ya ke aiki.
Kungiyar ta ce ba a bi ka’idar dokar NJC da dokar Babbar Kotun Abuja ta FCT HC ta 2003 ba.
“Ba za mu bari a maida harkar alkalanci hanyar dabbaka ra’ayin wasu manyan alkalai su na dora wadanda suka ga dama kuma a cikin ‘ya’yan su BA, alhali ba su cancanta ba.”
Sun kuma jaddada cewa akwai wadanda suka cancanta birjik ba a nemi su shiga jerin tantancewar ba, sai aka rakito ‘ya’yan mai shari’a wane d ‘yan gidan wance da wane.
“Da sun cancanta ma da dan dama-dama, to amma ko a tsarin dauka alkalanci a Babbar Kotun Abuja, ba su cancanta ba. An yi watsi da wadanda suka cancanta, ko damar shiga tantancewar ma ba a ba su ba.” Inji Odinkalu.