SOKOTO: Yadda Mahara suka kashe mutum sama da 50 ranar Sallah da ranar Alhamis

0

Wasu ‘yan bindiga a bisa babura da suka afkawa wasu kauyukan karamar Hukumar Sabon Birni, sun kashe akalla mutum 50 ranar Alhamis.

Maharan sun diran wa kauyukan Kuzari, Katumi, Masawa, da Dan-Aduwa ranar Sallah a daidai ana shagulgulan karamar Sallah sannan suka sake shigowa a karo na biyu cikin kwanaki 4 suka karkashe mutane son ran su.

Wani mazaunin daya daga cikin wadannan kauyuka dake kurkusa da juna ya ce maharan da suka diran musu sun fi su 100 a kan babura.

” Ko da suka shigo mana gari sun rika barin harsasai ne ta ko ina babu kakkautawa. Suna dirka wa duk wanda suka ci karo da shi dalma.

Ya ce a ranar Alhamis, sun bizne mutane akalla 50.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya nuna rashin jin dadin sa matuka bisa wannan mummunar hari da aka kai wa mutane basu ji ba basu gani ba.

Ko a ranar Lahadi da aka fara afkawa mutanen kauyukan, gwamna Tambuwal da Kwamishinan ‘yan sandan jihar sun Kai ziyara garuruwan domin gani wa kansu abin da ya faru.

A lokacin, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi wa al’ummar karamar hukumar alkawarin samar musu da tsaro domin kauce wa sake aukuwar hakan.

Sai gashi kwanaki hudu bayan haka maharan sun dawo sun tafka barnan da ta fi ta baya.

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa ‘yan uwan wadanda suka rasa nasu a harin.

Shugaba Buhari ya ce sojojin Najeriya za su lallasa wadanda suka aikata wannan mummunar aiki. Ya kara da cewa tuni zaratan dakarun Najeriya sun fara Shirin dirawwa wadannan ‘yan ta’adda domin gamawa da su.

” A wannan lokaci da ake fama da matsin Korona, wasu kuma da basu da tausayi su rika azabtar da mutane, gwamnati ba zata bari suna ci gaba da abinda suka ga dama ba, lallai za su dandana kudar su.

Share.

game da Author