Kungiyar Rajin Bin Diddigin Tabbatar da Ayyuka Bisa Ka’ida (SERAP), ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki bakwai ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya cikakken bayani dalla-dalla, na adadin tulin bashin da ya tattago wa kasar nan, tun daga ranar da aka fara rantsar da shi, 29 Ga Mayu, 2015 zuwa yau.
Sannan kuma SERAP ta nemi Buhari ya kafa binciken masu zaman kan su domin su zaluko adadin bashin da gwamnatocin baya suka ciwo, tun daga 1999 zuwa 2015.
SERAP na bukatar Buhari ya bayyana dalla-dalla ayyukan da ya yi da kudaden da ya rika ciwo bashi.
Kuma ya fadi wuri ko jihar da aka yi aikin da shekara da aka yi aikin da kuma adadin nawa aka yi kwangilar.
Haka nan kuma SERAP na so Buhari ya bayyana ayyukan da gwamnatocin baya suka yi da kudaden da suka ciwo bashi, kuma a bayyana wuraren da aka yi aikin.
“Mu na so Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da wannan lokacin da ya cika shekaru biyar a kan mulki, ya kara wa kan sa karsashi, ta hanyar bayyana yawan bashin da ciwo, tun daga hawan sa cikin 2015 zuwa yau.
“Kuma ya kafa masu bincikeasu zaman kan su su gano yawan bashin da gwamnatocin baya, tun daga 1999 suka ciwo. Hakan zai kawar da shakkun cewa duk sace kudaden aka yi, aka karkatar da su, kuma an jefa kasa cikin ukubar biyar bashin da babu rana ko shekarun da za a iya biya.”
Wannan bayani na cikin wasikar da SERAP ta rubuta ranar 30 Ga Mayu, kuma Mataimakin Darakta, Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu.
“Yawan bashin da gwamnatin ka ta ciwo abin tayar da hankali ne, domin a tarihi gwamnatocin da su ka ciwo bashin, sukan tafi su bar al’ummar kasar nan cikin halin kunci da alakakai.
“Ga shi kuma ana zargin cewa duk da tulin kudin da ake ciwowa da sunan bashi, babu wasu ayyukan da za a iya gani a ce kwalliya ta biya kudin sabulu.”
SERAP ta kara da cewa yawan cin bashin nan na neman jefa kasar nan rami gaba dubu, ta yadda hatta ma kudin yaki da cutar Coronavirus nema suke yi su gagari kasaitacciyar kasa kamar Najeriya.
Idan ba a manta ba, cikin wannan makon ne Majalisa ta amince wa Buhari ya ciwo bashin dala bilyan 5.51, domin cike gibin kasafin kudi na 2020.
Kwanan baya kuma Majalisa ta amince Buhari ya ciwo bashin naira bilyan 850.
Sannan kuma yanzu haka Majalisar Datyawa ta amince Buhari ya ciwo bashin dala bilyan 22.79. Amma batun ya na Majalisar Tarayya, ba ta kai ga amincewa ba tukunna.
SERAP dai ta bai wa Buhari kwanaki bakwai ya yi wannan bayani, ko kuma su hadu a kotu.
SERAP daga karshe ta shawarci Buhari ya nabba’a, ya daina giringidishin saurin ciwo bashi.
Kungiyar ta ce a matsayin sa na shugaban kasa, kamata ya yi a wannan mawuyacin halin da ake ciki, ya fito da hanyoyin rage kashe kudade barkatai.
Musamman kungiyar ta yi kira a soke nai wa tsoffin gwamnonin kasar nan kudaden fansho, domin a ko yaushe tsoffin gwamnonin kara yawa suke yi, kuma sai narka musu kudaden yin bushasha kawai gwamnatocin jihohi ke yi.
Discussion about this post