Sarkin Rano, Alh Tafida Abubakar Illa ya rasu

0

Maimartaba Sarkin Rano, Tafida Abubakar Illa ya rasu.

Sarki Tafida ya rasu a asibitin Nasarawa da ke birnin Kano bayan fama da yayi da rashin lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 75.

Sakataren masarautar Rano, Sank Haruna ya tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar maimartaba.

Duk da ba a bayyana ciwon da ta yi sanadiyyar mutuwar sarki Tafida.

Rano daya ce daga cikin sabbin masarautan da gwamnan jihar Kano ya kirkiro.

Allah yaji kan sa Amin.

Share.

game da Author