Sarautun da marigayi Yusuf Bayero ya yi kafin Allah yayi masa rasuwa a Kano

0

Marigayi Dan-Iyan Kano Yusuf Bayero ya rasu ranar Lahadi 10 ga watan Mayu, 2020.

Marigayin ya rasu bayan fama da yayi da rashin Lafiya. Kafin rasuwar sa shini Dan-Iyan Kano, hakimin dawakin Kudu.

An yi jana’izar marigayi dan-iya Yusuf ranar Lahadi a Kano. Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero duk sun halarci jana’izar sa.

Ya rasu yana da ‘ya’ya tara, mata daya da dangi.

Marigayi Yusuf Bayero ne barasake na uku da ya rasu a Kano cikin mako guda baya ga Sarkin Rano, Marigayi Tafida Abubakar Ila da marigayi Isa Hashim (Jarman Kano).

Marigayi Yusuf Bayero ya rike sarautun Dan Ruwata kuma hakimin Ajingi, Dan Ruwata kuma hakimin Bichi, sannan ya rike sarautun Dan Isa, then Dan Buram da Barde. A 1993 aka nada Dan-Iya kuma hakimin Dawakin Kudu.

Ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Share.

game da Author