Sannu a hankali za mu janye dokar Zaman Gida Dole a Kano – Ganduje

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa sannu a hankali gwamnatin jihar za ta janye dokar hana walwala da zaman gida dole da ta saka.

Ganduje ya ce duk da mutane suna so ya saki kowa ya ci gaba da al’amurorin su, dole kuma a duba yanayin yaduwar cutar a jihar, domin abu uku ne dama ” Ko dai rayuwa, ko kuma a kyale mutane su ci gaba da al’amurorin su ko kuma a ba kowa dama.

Ya kara da cewa ko a kasashen duniya ana shakun ci gaba da garkame gari kwata-kwata, babu zirga-zirga a yanzu.

” Amma kuma abinda nake so in shaida wa jama’a shine dole dai wata rana a janye dokar. ”

Bayan haka kuma suma kwamitin dattawan Kano sun yi alakwarin ci gaba da taimakawa gwamnan jihar akan wannan aiki da ya sa a gaba na dakile yaduwar cutar Korona a jihar.

Share.

game da Author