Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya gargadi ‘yan majalisa da su rika jaddada bin doka maimakon karya doka da suke yi a majalisa na gwamutsuwa da juna da suke yi.
Lawan yayi kira ga sanatoci da su rika zama nesa-nesa da juna kamar yadda aka yi horo da a rika yi amma kuma basu yi.
Sannan kuma ya hore su da su rika saka takunkumin fuska a duk lokacin da za su shigo majalisa.
” Ina rokon ku da mu rika bin doka kamar yadda aka saka a majalisa.
Idan ba a manta Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya karanta wasikar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Zauren majalisar Dattijai ranar Talata.
A wasikar Buhari ya roki majalisar ta amince da sunayen jakadu 42 da yake so ya nada a kasashen duniya.
Ga sunayen su C. O Nwachukwu (Abia), A. Kefas (Adamawa), R. U Brown (Akwa Ibom), G. A, Odidibo (Anambra), O. C Onowu (Anambra), Y. S Sulieman (Bauchi), E. S Agbana (Bayelsa), B. B.M Okoyen (Bayelsa), G. M Okoko (Benue), A. M Garba (Borno), M. I Bashir (Borno).
Others are, M. O Abang (Cross River), A. E Alote (Cross River), G. E Edokpa (Edo), A. M Maduwike (Enugu), Adamu Lamua (Gombe), Innocent Iwejuo (Imo), A. S Abubakar (Jigawa), Y. A Ahmed (Jigawa), S. D Umar (Kaduna), A. A Sule (Kano), G. Y Hamza (Kano), N. Rini (Katsina), Ahmed Rimawa (Katsina), M. Manu (Kebbi) and I. R Ocheni (Kogi).
I. A Yusuf (Kogi), M. Abdulraheem (Kwara), W. A Adedeji (Lagos), A. U Ogah (Nasarawa), A. A Musa (Niger), N. A Kolo (Niger), H. O Olaniyon (Ogun), A. R Adejola (Ogun), O. E Awe (Ondo), O. O Aluko (Osun), E. A, Alatishe (Osun), V. A Adeleke (Oyo), M. S Adamu (Plateau), I. N Charles (Rivers), M. Ifu (Taraba), B. B Hamman (Yobe).
Bayan haka shugaba Buhari ya aiak da sunaye biyu domin majalisa ta amince da su darektocin hukumar NDIC.
An aika da sunayen Diana Okonta (Kudu Maso Kudu) Yiana Kali (Arewa Maso Gabas).
Bayan haka kuma Buhari ya aika da sunayen mambobin hukumar NLRC. Wadanda aka nada sun hada da Jummai Audi, Shugaba; Edele Chima, Kwamishina; Bassey Dan, Kwamishina da Mohammed Ibrahim, Kwamishina.