Zuwa Ga Masu Karanta PREMIUM TIMES
Sanin kowa ne cewa Najeriya ta afka cikin matsalolin tattalin arzikin kasa bayan farashin danyen mai a duniya ya yi faduwar-‘yan-bori, kasafin kudi na 2020 ya kakare, sannan kuma annobar Coronavirus ta kara yi wa tattalin arzikin dukan-farat-daya.
A irin wannan mawuyacin hali da zaman dar-dar ana bukatar nagartacciyar kafar yada labarai mai bayar da labaran abin da ke faruwa akai-akai. To irin wannan lokaci samun irin haka sai fa jaridar da ta tsaya tsayin daka wajen fadar gaskiya, sanin darajar kan ta da kuma tantance sahihancin bayani komai rintsi, cikin kwarewar aiki da nagarta.
Babu ko tantama, wannan lokaci jaridu na cikin halin kaka-ni-ka-yin da ya zame musu barazanar yiwuwar durkushewa. To kuma sai barkewar cutar Coronavirus ta kara dagula komai.
Yayin da ake fuskantar sallamar ma’aikata, rage wa ma’aikata albashi da bin wasu hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, ita kuwa PREMIUM TIMES ta aminta da cewa za ta ci gaba da dorewa a sahihiyar hanyar da tun fil azal aka kafa ta a kai. Domin yin ratse a saki hanya ce ke sa a taka kaya. Mu na nan kan turbar mu ta kare gaskiya, kare kalubalen da al’umma ke fuskanta da kuma dabbaka ingantacciyar dimokradiyya.
Jajircewar da PREMIUM TIMES ta yi wajen bin sahihiyar turbar aikin jarida, rashin cusa siyasa ko bangaranci, rashin bada kai borin ya hau da kin yarda da rufa-rufa, su ne su ka sa wannan jarida ce daya tilo a tarihin Najeriya da ta taba samun Lambar Girmamawa ta Pulitzer Award, lambar gwarzuwar jarida mai binciken kwakwaf, One World Award da Shining Light Award.
Cikin watan Afrilu gwarzon masanin tattalin arziki, Joseph Stiglitz, wanda ya lashe kyautar Nobel ta duniya, ya bayyana cewa Babban Editan PREMIUM TIMES, Misikilu Mojeed na daya daga cikin ‘yan jaridar da ya ke tutiya da su a duniya. Wannan yabo da jinjina ya nuna yadda wannan jarida ta ciri tuta a fadin Afrika wajen jajircewa kan zakulo bayanai da binciken kwakwaf, ta yadda ba mu da ta biyu a wannan nahiya.
Masu iya magana sun ce ‘tafiya da gwani mai dadi’, to amma irin wannan tafiya a cikin mawuyacin hali, to fa ta na bukatar kudi.
Dalili kenan mu ke kira ga masu karatun mu da sauran abokan zumunci su zuba wata ‘yar gudummawa a cikin asusun inganta dorewar wannan jarida a cikin kimar ta da martabar ta, tare da jajircewa wajen tsayawa kare tsaron kasar nan, gaskiya, binciken kwakwaf da kuma bibiyar shugabanni mu tabbatar su na bin sahihiyar dimokradiyya, kuma mu ci gaba da ragargazar mulkin kama-karya.
Mun gode,
Dapo Olorunyomi
Fa’idojin zama dan Kungiyar masu karatu na ‘PT’ Membership Club
1. Garabasar Bayanan Wata-wata: Za a rika samun bayanan Karin haske kan labaran da su ka kunshi siyasa, kasuwanci, cinikayya da tattalin arziki, al’adu, kiwon lafiya da binciken kwakwaf.
Akwai kuma bayanai da labarai na nasarorin da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje suka samu a duniya. Sannan kuma mamba zai samu damar sanin yadda mu ke gudanar da ayyukan mu a saukake ko daga ina ya ke.
2. Mamba zai samu damar gayyata zuwa halartar kasaitattun tarukan da PREMIUM TIMES ke shiryawa a kowace shekara, da suka hada har da Taron Kiwon Lafiya, Taron Harkokin Noma, kaddamar da littattafai, taron nuna fasaha da kuma taron halartar kasaitacciyar walima tare da mashahuran mambobin mu. Za a biya dan tukuici daidai karfin aljihun kowane mamba.
3. Mamba zai samu damar yin wata ganawar musamman duk wata tare da wakilai da Editocin mu, a Dandalin Zumunta na Twitter. Kuma akwai kuma taron duk bayan watanni uku. Sannan mamba zai iya bukatar kebantaccen zaman walimar musamman ya gana da editocin mu, a duk lokacin da ya samu damar haka a Abuja.
4. Mamba zai samu garabasar samun rahusar farashin littattafan da kamfanin PREMIUM TIMES ke bugawa.