Shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates, ya bayyana cewa za a iya samun maganin rigakafin cutar Covid-19 nan da shekaru biyu ko kuma idan an yi sauri nan da watanni 9 masu zuwa.
Gates ya ce a yanzu haka masana kimiyya na gudanar da bincike kan magunguna 115 domin samun mafi ingancin maganin warkar da cutar.
Ya kuma ce magunguna 10 daga cikin wadanda aka yi bincike akai sun fara nuna alamun ingancin warkar da cutar.
“Duk da haka gidauniyar Gates za ta sa ido domin samun maganin warkar sa cutar da ya fi dacewa.
Ya kuma jinjina wa kokarin da masana kimiyya ke yi wajen yin maganin musamman yadda suke kokarin ganin sun sarrafa maganin cikin shekaru biyu ko kuma kasa da haka.
“Bisa ga sharuddan sarrafa magani kamata ya yi ya dauki tsawon shekaru biyar kafin a samu ingantaccen magani.
“Kafin a samu ingantaccen magani dole sai an samu tabbacin yawan maganin da ya kamata mutum ya sha.
Gates ya ce duk wadannan matsaloli an kawar da su domin gwamnatocin kasashen duniya da gidauniyar Gates sun hada hannu domin ganin an kawar da duk wadannan matsaloli.
Cutar coronavirus ta bullo a kasashe 185 inda sama da mutum miliyan sun kamu da cutar.
Daga ciki mutum sama da 200,000 sun mutu.
Haka kuma Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 206 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.
A bayanan da NCDC ta fitar Jihar kano ta samu karin mutum 80, 45-Legas, 12-Gombe, 9-Bauchi, 9-Sokoto, 7-Borno, 7-Edo, 6-Rivers, 6-Ogun, 4-FCT, 4-Akwa Ibom, 4-Bayelsa, 3-Kaduna, 2-Oyo, 2-Delta, 2-Nasarawa, 1-Ondo, 1-Kebbi
Yanzu mutum 1932 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 319 sun warke, 58 sun mutu