Rundunar ‘Yan sandan Katsina ta tsare dattijo mai shekara 70 saboda ya zagi Buhari da Masari

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tsare wani dattijo mai shekara 70 don yayi kalaman batanci ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Aminu Masari.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar, Gambo Isah, ya bayyana cewa an Kama wannan dattijo bayan gani da akayi a wani bidiyo da ya karade shoshiyal midiya yana surfa wa Shugaba Buhari zagi da gwamna Masari.

Shi dai wannan dattijo mai suna Lawal Izala ya ce ya fusata ne bayan ya dawo daga kauyen su Inda ya iske mahara sun sace musu shanu sannan sun karkashe mutane.

A dalilin haka ne ya rika aman zafafan kalaman batanci yana sukan salon mulkin Shugaba Buhari da Gwamnan jihar Aminu Masari.

Bayan Lawal Izala, an tasa keyar wasu mutum biyu da ake zaton sune suka dauki wannan dattijo a lokacin da yake surfa wa Buhari da Masari zagi suka yada a yanar gizo.

Dukkan su sun musanta cewa sune suka saka bidiyon a shafin yanar gizo. daya daga cikin su ya ce bayan sun dauki wannan bidiyo ya rabawa a abokansa da suke tare a wannan wuri. Ya ce kila wani daga cikin su ne ya saka a shafin yanar gizo.

Sai dai Gambo Isah ya ce ‘yan sanda za su hukunta wadannan mutane domin abinda suka yi saba doka ne.

Share.

game da Author