Oshiomhole ya kamo hanyar kashe APC a Edo, irin kisan da ya yi mata a Bayelsa, Zamfara, Ribas – Obaseki

0

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, ya maida wa Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole raddin cewa a Edo ake zaben takarar fidda gwani, ba a Abuja ba.

Hakan ya biyo bayan da wasu ‘yan takarar kurejar gwamna a karkashin APC su bakwai sun janye wa dan takara daya, Eze Iyamu a matsayin wanda suka ce sun tsayar.

Wadanda suka janye din da wanda aka janye wa, duk magoya bayan daya bangaren APC ne mai goyon bayan Adams Oshiomhole a dambarwar siyasar Jihar Edo.

Cikin wata takarda da Kakakin Yada Labarai na Obaseki, Crusoe Osagie ya fitar, Obaseki ya ce harda-hardar mugunyar siyasar da Oshiomhole ke kitsawa a Edo, za ta iya janyo wa jihar asara irin wadda ya janyo APC ta rasa wasu jihohi kamar Bayelsa, Rivers, Zamfara da sauran su.

“Oshiomhole ya sani cewa shirmen da ya kulla a Abuja, bulkara ce kawai, domin a Jihar Edo ake fitar da dan takara, ba a Abuja ba.

” Kwamacalar da Oshiomhole ke kitsawa abin takaici ne ga jam’iyyar APC kuma zubar da kimar Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi.

“Mu dai abin da muka sani shi ne sai ranar 22 Ga Yuni za a yi zaben fidda gwanin ‘yan takarar gwamna. Kuma a Edo za a yi, ba a gidan wani gogarma a Abuja ba.

“Don haka duk ma wani abu sa suka kulla, ba mai dorewa ba ne. Domin idan ma ba su sha kaye ba a wurin zaben fidda gwani, to kotu za ta kunyata su.”

Bayan ‘yan takara sun janye wa Iyamu, ya zarce hedikwatar APC ya saki fam na takarar gwamnan jihar Edo a karkashin APC.

Hakan ya na nufin kenan au biyu shi da Obaseki za su yi takara a zaben fidda gwani.

Adams Oshiomhole ba ya ga-maciji shi da Gwamna Obaseki, mutumin da ya daure wa gindi ya zama gwamna bayan ya kallama wa’adin sa ba shekaru takwas.

Obaseki ya danganta raba hanyar da ya yi shi da Oshiomhole cewa, saboda kawai ya ki yarda ya zama dan-amshin-Shatan Oahiomhole, shi ya sa sabani ya shiga tsakanin su.

Share.

game da Author