Hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu a matsayin ranar sallamar daliban da suka kammala ayyukan Yi was kasa hidima.
Kakakin hukumar Adenike Adeyemi ta sanar da haka ranar Litini a wani takarda da aka raba wa manema labarai.
Adeyemi ta ce a wannnan rana Hukumar za ta raba satifiket din kammala bautar kasa ga daliban da suka kammala hidiman su a hedikwatan kananan hukumomin da suka yi hidimar su kasa.
Ta kuma ce ba za a yi paredi ba Ko kuma wani taro kamar yadda aka saba yi ba.
Adeyemi ta ce Hukumar za ta dauki kwanaki 10 domin rabawa dalibai satifiket din su.
Ta ce ga daliban da basu zama a jihohin da suka yi bautar kasa za su iya karbar satifiket din su bayan an janye dokar hana tafiye-tafiye.
Hukumar NYSC ta dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar cutar coronavirus sannan da gujewa wa karya dokokin da gwamnati ta saka domin dakile yaduwar cutar.
Za a iya ziyartan shafin Hukumar a yanar giz domin samun karin bayani.
Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Maris ne Hukumar NYSC ta dakatar da horas da dalibai masu yi wa kasa hidima na Rukunin A na shekarar 2020 a duk sansanonin Najeriya.
Hukumar ta kuma rarraba wa daliban wasikun tura su wuraren da za su yi aikin yi wa kasa hidimma Kai tsaye.
NYSC ta yi haka ne domin hana yaduwar cutar coronavirus a kasar.
Discussion about this post