Najeriya ta dakatar da kwaso wadanda suka makale a kasashen waje

0

Gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da aikin kwaso ‘yan kasar nan da suke makale a wasu kasashe, sakamakon hana zirga-zirgar jiragen sama, bayan barkewar cutar Coronavirus a duniya.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da kwamitin yaki da Coronavirus ke yi da ‘yan jarida, kowace rana a Abuja.

Ya ce an dakatar da shirin ne domin sake tsarin sa gaba daya, ta yadda za a samu saukin kwaso su a saukake da kuma maida kowa gidan sa a saukake.

Sabbin Ka’idoji:

1. Duk wanda za a kwaso ko ma daga wace kasa ne, sai ya yi gwajin cutar Coronavirus daga can kasar da ya ke tukunna.

2. Ya tabbatar ya yi gwajin kwanaki 9 zuwa kwanaki 5 kafin ranar da za a dauki shi.

3. Wanda gwaji ya nuna ba shi dauke da cutar Coronavirus kadai za a dauko.

4. Idan gwaji ya nuna ka na dauke da Coronavirus, to ba za a bari ka hau jirgi zuwa Najeriya ba.

5. A nan Najeriya, za a daina killace su a otal tsawon kwana 14.

6. Za a yi wa kowa gwaji idan ya sauka. Daga nan ya zarce zuwa gida.

7. Idan ya isa gida zai killace kan sa har sakamako ya fito.

8. Idan an same shi da cutar Coronavirus, to za a dauke shi a killace can a cibiyar killacewa.

9. Idan ba shi dauke da cutar Coronavirus kuwa, shikenan, sai sam-barka.

Idan ba a manta ba, Najeriya ta fara jido ‘yan kasar ta daga Amurka, Birtaniya, Saudi Arabiya da sauran kasashe, kafin wannan sanarwar dakatarwa.

Akalla mutum 11,000 za a maido daga Saudiyya, wadanda yawancin su tikari ne da ‘yan agulla, wadanda ke zaune a kasar ba da iznin hukuma ba.

Share.

game da Author