Najeriya ta bayyana kudirin ta na tallafa wa kafafen yada labarai domin ci gaba da gudanar da ayyukan su a lokacin zaman kuncin Coronavirus da kuma bayan dakile cutar.
Ministan Yada Labarai Kai Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayani a wurin taron manema labarai da ake gudanarwa a kullum dangane da ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar Coronavirus a Abuja.
Ya ce Gwamnatin Tarayya na sane da halin da kafafen yada labarai ke ciki a kasar nan, don haka ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen fito da wani tsarin tallafawa gare su domin farfadowa da warware wa.
Kai Mohammed ya ce a na kan kokarin fito da tsari da hanyar tallafa wa kafafen da kudade domin su dore wajen gudanar da ayyukan su.
“A jiya an yi taro dangane da lamarin a Lagos, kuma ana kan hanyar kafa kwamitin da zai tantace abin da ya dace a yi. Kuma ana kan tantance sunayen da suka kamata a saka a cikin kwamitin.
“Nan ba da dadewa ba da an kamalla komai za mu sanar da sunayen ‘yan kwamiti da kuma nauyin aikin da aka dora musu.
Annobar Coronavirus da ta barke a duniya ta durkusar da kamfanoni da masana’antu, cikin har da wasu kafafen yada labarai manya a duniya.
Nan a Najeriya kafafen da dama, musamman na radiyo na fuskantar durkushewa.
Discussion about this post