Ministan Lafiya, Osagie Ehanire. Ya bayyana cewa binciken su ya tabbatar da cewa kashi 70 bisa 100 na wadanda Coronavirus ta kashe a Najeriya, su na da kwantaccen ciwon da ke damun su, kafin Coronavirus ta karasa su.
Ya ce yawancin su duk su na da ciwon hawan-jini da ciwon sugar tun kafin su kamu da cutar Coronavirus.
Da ya ke magana a wurin taron manema labarai domin sanar da irin ci gaban da Kwamitin Yaki da Coronavirus (PTF Covid-19) ke samu, Minista Ehanire ya ce sauran cikon kashi 30 bisa 100 kuma masu fama da ciwon koda ne da kanjamau, kansa, tarin TV da sauran ciwace-ciwace.
“Kashi 70 bisa 100 a cikin su kuma duk datttawan da suka haura shekara 60 ne.
“Sannan kuma kashi 1 bisa 2 na wadanda suka mutu, duk a gida suka mutu. Sannan kuma kashi 50 cikin 100 din su duk na su nuna wata alama a jikin su da ke bayyana cutar Coronavirus ba.”
Ehanire ya kara da cewa jama’a da sun ji kyas, to su garzaya a gwada su. Kuma duk wanda aka dauki gwajin sa, ya rika gaggauta killace kan sa kafin sakamako ya fito.
Ya ce samun kawar su barkewar cutar sai da hadin kan jama’a.
Ana dai ci gaba da nuna damuwar yadda jama’a da dama ba su bari a gwada su, wasu kuma ba su yarda a gano inda su ke, ballantana a killace su.
Hukumar NCDC kuma ta nuna damuwar yadda ake ci gaba da karin samun masu kamuwa da cutar ganin yadda suka doshi 7,000 kuma a cikin kwanaki hudu aka samu mutum sama da 1,000.
Discussion about this post