Tsohon Gwamnan Jihar Barno, Ali Sheriff ya karyata zargin da ake masa cewa ya ji zuwa a yi masa gwaji, bayan ya yi mu’amala da mutanen da cutar Coronavirus ta kashe.
Cikin makon jiya ne aka rufe gawar mahaifin Ali Sheriff a Maiduguri. Jama’a da dama sun yi cincirindo wurin jana’iza, cikin har da daya tsohon gwamnan Barno, Mohammed Goni, wanda mako biyu bayan rasuwar mahaifin Sheriff, Goni ya mutu sakamakon cutar Coronavirus.
Sahara Reporters ta buga cewa Modu Sheriff na daya daga cikin wasu fitattun mutane biyu da Kwamitin Yaki da Coronavirus na Jihar Barno ke nema da suka yi mu’amala da mamacin cutar Coronavirus.
Sai dai kuma Sheriff ya karyata rahoton da Sahara Reporters ta buga, ya ce ba shi da tushe ballantana makama.
Cikin wata takarda da kakakin yada labarai na Sheriff ya fitar, ya ce, “ba gaskiya ba ne da Sahara Reporters ta buga lanarin cewa marigayi Sarkin Bama da ya rasu dalilin Coronavirus ya halarci Jana’idar mahaifin sa.”
Yayin da Sheriff ya musanta halartar na tsohon sarkin, amma bai karyata halartar marigayi Goni ba, wanda shi ma ya rasu makonni biyu bayan rasuwar mahaifin Sheriff.
PREMIUM TIMES ta tuntubi Kwamishinan Yada Lanarai na Jihar Borno, kuma dan Kwamitin Yaki da Coronavirus a jihar dangane da ko.sun gayyaci Sheriff amma ya ki zuwa ko ya ki bari a yi masa gwaji?
Sai kwamishina ya ce shi dai a iyakar sanin sa, kwamitin su bai gayyaci Sheriff ko neman zuwa a gan shi domin a yi masa gwaji ba.
Sheriff wanda tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ne, ya ce bai taba kokarin maida wa yaki da Coronavirus hannun agogo baya ba. Ya ce shi tun ma tuni ya janye jikin sa daga jama’a, ya na kaffa-kaffa da shiga mutane.
Discussion about this post