Kungiyar kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya wa Allah ya sassauta dokar hana zuwa wuraren bauta da aka garkame a jihar saboda annobar Korona sama da wata daya.
Shugaban Kungiyar na Kaduna John Hayab ne ya yi wannan kira ranar Talata a wani takarda da ya raba wa manema labarai.
Hayab ya ce baiwa musulmai da kiristoci damar haduwa a masalatai da coci -coci zai taimaka wajen kara wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin da ya kamata a kiyaye don kada a kamu da cutar.
” Muna rokon gwamna El-Rufai ya sassauta dokar hana zuwa masallatai da coci-coci a jihar Kaduna. Muna kuma tabbatar masa idan ya bamu wannan dama za mu tabbata mabiyan mu suna bin doka sau da kafa.
” Za mu samar da bukatan ruwa na wanke hannu da sabulu sannan kuma da man tsaftace hannaye a wuraren bautar mu kuma mu rika kwadaitar da mabiyanmu game da hanyoyin da za abi wajen kare kai daga kamuwa da cutar.
Hayab ya kara da cewa gwamna ya dube su da idon tausayi ya bari ana sallar juma’a da zuwa Coci ranar Lahadi.
” Bayan haka ko wajen taimakawa marasa karfi, a wuraren ibada za a san wadanda ke da bukata da kuma wadanda suka cancanci taimako a taimak musu cikin gaggawa. hakan zai taimaka wa gwamnati a wajen raba kayan tallafi.
A karshe ya yaba wa gwamna El-rufai bisa kokarin da yake a jihar tun da aka bayyana bullowar cutar a jihar da koma dokokin da ya saka domin kare lafiyar mutanen Kaduna.
Jihar Kaduna na da mutum sama da 100 da suka kamu da cutar Coronavirus a jihar.
A jawabin da El-Rufai yayi ya wa ‘yan jihar ranar Talata ya ce ba zai sassauta dokar hana walwala a jihar Kaduna ba sai an samu saukin al’amura game da cutar.