Muma fa Almajiran da ake dawo mana dasu Kano wasunsu na da Coronavirus, amma wasu sun maida abin siyasa – Ganduje

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi kira da kakkausar murya da adaina maida kokarin dakile yaduwar Coronavirus da ake yi musamman a yankin Arewa siyasa.

Ganduje yace maganar kowa yace daga Kano Almajirai suka shigo masa da Coronavirus, bai kamata ba domin ita ma Kanon fa an dawo mata da Almajirai da dama kuma duk suna dauke da coronavirus daga wasu jihohin.

” Mun amince a kungiyar gwamnoni cewa duk wani Almajiri da yake wata jihar a maida shi jiharsa ta Asali. Kuma dalilin da ya sa kowacce jiha ke kokarin maida Almajirai zuwa jihohin su na Asali kenan.

” Muma fa Almajiran da ake dawo mana da su wasun su na dauke da Coronavirus, amma bamu cewa komai, sannan ba mu yin siyasa dashi ko kuma neman suna. Mu mun san cewa ba haka suke bukata ba a yanzu, kula da ji dasu suke bukata.

” Kamar yadda muke maida wasu almajirai jihohin su na asali haka muma ake dawo mana da namu almajiran, kuma da yawa daga cikin su akan samu suna dauke da cutar Coronavirus idan aka yi musu gwaji, amma ba mu shela, siyasa akai ko neman suna da su.

” Mutane su sani cewa wadannan yaran ba a lokacin da ake maida su jihohin su na asali ne suke kamuwa da wannan cuta ba. Saboda haka kada wasu su cika mu da surutu. Hakan ma dai anayi ne don bin umarnin kungiyar gwamnonin, amma ba wai don a burge wani ba. Wannan shine gaskiyar magana.

Ita ko jihar Jigawa har yanzu bata maida koda Almajiri daya ne zuwa jiharsa ta Asali ba. Gwamnatin tace ta ki yin haka ne saboda kada a yada cutar zuwa wasu jihohi. Tace gara a barsu tukunnan a nema musu magani.

Ko gwamnatin tarayya ta koka kan wannan jigila da ake yi na Almajirai daga jihohin kasar nan cewa hakan na dada yada cutar a Kasar nan.

Share.

game da Author